Zuwa ga Nasir El-Rufai

Mun wayi gari cike da mamaki ganin yadda ka dage akan wannan canjin kudi da sunan nema wa talaka sauki. Abin tambaya anan shine, wani talakan kake nufi, wanda baka san yana wahala ba sai yanzu da akayi abinda ya shafe ka kai tsaye?

Kana nufin tun 2015 talaka bai taba shiga damuwa ba sai yanzu?

Idan don talaka kake wannan abu;

1. Meyasa baka kai karan gwamnatin tarraya akan matsalar rashi tsaro daya addabi arewa (ciki harda Kaduna) ba? Ko ba talaka ake kashewa ba?

2. Meyasa baka kaisu kara akan garkuwa da mutane  da ake ta fama dashi a hanyoyi da garuruwan jihar Kaduna ba?

3. Meyasa duk wahalan man fetur da talaka keyi baka kai kara ba?

4. Meyasa ka rushe ma talakawa shagunan ka sayar wa masu kudi yan’uwanka?

5. Meyasa ka hana talakawa cinikayya a kan tituna domin neman abinci?

6. Meyasa ka kori talakawa da hannunka daga ayyukan gwamnati mabambanta?

7. Meyasa ka rushe ma talakawa muhalli ba tare da rage masu radadi ba?

8.Meyasa ka kara kudin makaranta a KASU wanda ya’yan talakawan jihar Kaduna ke samun saukin karatu?

Ko kana nufin canjin kudi yafi duk wadannan shafan talaka?

Daga Malam isa Abbas Ahmad

Dauka Daga Facebook

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here