Gwamnatin Tarayya ta Ceto ‘Yan Najeriya 101 Daga Libya
Gwamnati ta ceto yan Najeriya 101 daga rikicin Libya.
Daga cikinsu akwai iyalan tsofaffin ‘yan ta’addan ISIS dake kasar Libya.
An tabbatar da dukkansu babu mai cutar corona kafin bari su shigo Najeriya.
Abuja – Gwamnatin tarayya ta shigo wasu ‘yan Najeriya 101 daga kasar Libya, cikinsu akwai iyalan ‘yan ta’addan ISIS 22 da aka kashe yayin yaki.
Wadannan mutane sun dira birnin tarayya Abuja ne ranar Juma’a, rahoton Punch.
Read Also:
Wannan na kunshe cikin jawabin da shugaban sashen labaran hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje NIDCOM, Abdur-Rahman Balogun, ya saki ranar Asabar.
Sun samu kyakkyawan tarba daga jami’an ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, NIDCOM, hukumar kiyaye yaduwar cututtuka, hukumar yakan muggan kwayoyi, hukumar agaji na gaggawa, hukumar DSS, hukumar shiga da fice da hukumar tashar jiragen ruwa.
Wani sashen jawabin yace:
“Wadannan yan Najeriya sun hada da iyalan tsaffin yan ta’addan ISIS 22 da aka kashe a Libya tare da yaransu.”
“Babu mai cutar Korona cikin dukkansu kuma sun dira daidai karfe 10:15 na dare a tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe Abuja, cikin jirgin Airforce C130.”