China da Taiwan: Rashin Jituwa Tsakanin Kasashen 2 ya Kara Tsanani Cikin Shekaru 40

 

Rashin jituwa tsakanin China da Taiwan ya yi tsanani a cikin shekaru 40, a cewar ministan tsaron Taiwan din, inda ya yi gargadin cewa hakan na iya haifar da hari tsakanin bangarorin biyu.

Kalaman Chiu Kuo-cheng na zuwa ne bayan da China ta aika wasu jiragen yaki sararin samaniyar Taiwan tsawon kwanaki hudu a jere.

Taiwan na ganin kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta. Sai dai China na ganin Taiwan a matsayin yankin da ya balle.

Duk da cewa jiragen yakin Chinar ba su shiga har cikin tsibirin ba, Mista Chiu ya yi gargadin cewa akwai hatsarin kai hari bisa kuskure.

Haka kuma, Mista Chiu ya yi gargadin cewa China na iya shiga kasar don kaddamar da cikakken yaki a tsibirin kawo shekarar 2025.

Ya yi magana ne a lokacin wani taron kwamitin majalisar dokoki a Taipei kan kashe kudi don samar da tsaro wajen gina makamai masu linzami da jiragen yaki.

Ya ce China na da damar shiga yaki, kuma ya ce matakin na iya kara yin sauki a shekaru masu zuwa sai dai bai yin karin bayani kan abin da yake nufi da hakan ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here