TMG, TI da CISLAC Sun Bukaci INEC ta Sake Duba Sakamakon Zaɓe a Inda Aka Tafka Maguɗi
Zaɓen da ya gabata cike yake da sayen ƙuri’a da musgunawa masu kaɗa kuri’a a cikin ƙasa. BVAS tayi aiki mai kyau.
Rahoton “Transparency International” yayi nuni da tsaro yayi ƙaranci.Inda sukace , zaɓen na 2023, shine zaɓe mafi samun rikita rikita a tarihin baya bayan nan.
Gamayyar ƙungiyoyin, sun bukaci a duba duk wani sakamakon zaɓe da aka tabbatar da an aikata “Ba daidai ba”
Zaɓen Najeriya yazo ya tafi yatafi yabar baya da ƙura.
Masu riba sun ƙirga riba, masu faɗuwa kuma sun amshi sakamakon su da hannun hagu.
Sai dai daga daya ɓari guda, INEC na fuskantar matsi akan zaɓen gama gari na 2023 da aka kammala a inda aka tabbatar da an tafka maguɗi.
Kungiyoyin da suke wannan kira sunyi kira ga hukumar data tabbata an samu shaidu sahihai dake nuni anyi maguɗi, sayen ƙuria tare da hana masu kaɗa kuri’a hakkin su na ƴan ƙasa kafin suyi wannan aikin.
Ƙungiyoyin da suka yi wannan kira sun haɗa da “Transition Monitoring Group (TMG)”, da “Transparency International (TI)” sai kuma “Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC)”.
Jaridar Leadership ta ruwaito yadda Shugaban ƙungiyoyin, Awwal Musa Rafsanjani, yace INEC ta duba sakamakon zaɓen musamman na wajen da aka tabbatar da anyi maguɗi.
Ƙungiyoyin suka ce:
Read Also:
“Dole ne INEC ta sake duba ga shaidun da aka miƙa mata na ba daidai ba,” Inji Rafsanjani.
Kungiyoyin suka ce, rashin tsaro, musgunawa masu kada kuri’a, sayan ƙuria sune siffa da za’a iya alaƙanta zaɓen da aka kammala na gwabnoni.
A yayin gudanar da zaɓen, ƙungiyoyin sunce sun jibge masu saka ido guda 768 a cikin ƙananan hukumomi guda 768 na cikin Najeriya.
Sunyi hakan ne badon komai ba, sai don su sanya ido akan zaɓen gwamnan da akai na 18 ga watan Maris.
A cewar rahoton ta bakin Rafsanjani:
“Yayin gudanar da zaɓen, mun samu rahoton takurawa masu kaɗa kuri’a, musgunawa, da kuma kalamai na cin zali da suka fita daga bakunan yan amutun manya manyan yan siyasa a ƙasar gabaki ɗaya.”
“Gazawar jami’an tsaron mu wajen kamawa da hukunta waɗanda suke waɗancan kalamai yasa suka ƙara ƙaimi wajen ci gaba da aikata irin kalaman a ranar zaɓe”.
Ƙungiyoyin sun sanar da cewa, zaɓen na 2023, zaɓe ne da yasa shakku a zuciyar mutane, biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa, wanda hakan yasa aka samu ƙarancin masu fitowa wajen kaɗa kuri’a.
Saboda haka ƙungiyoyin suka yi kira ga INEC da cewar:
“Dole ne INEC ta duba duk wani shaida da aka gabatar mata na dai-dai ba. EFCC da ICPC suci gaba da aikin su mai kyau wajen rage adadin siyan kuri’a, tare da kama su, daga siyan, ƴan tsakiya da kuma masu amsar kuɗin yayin gudanar da zaɓen”.