Mutane 25 Sun Rasa Rayukansu Sanadiyar Hatsarin Mota a Bauchi

Haɗarin ya faru ne akan hanyar Hadeja-Potiskum ta zuwa ƙaramar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi.

Direban motar ya rasa yadda zai sarrafa motar ne, wanda hakan yasa ya aukawa wasu mutane 11 dake hutawa a ƙarƙashin wata bishiya.

Hukumar FRSC ta Bauchi tace hatsarin ya faru ne saboda taƙe motar da akayi da kaya masu yawa, da gudun wuce sa’a, da yasa tayar motar ta fashe.

Bauchi- Idan ajali yayi kira ko babu ciwo dole aje. Mutuwa kenan, mai raba bawa da rai, bawai don baya so ba.

Ita mutuwa ko babu ciwo idan lokaci yayi, tafiya akeyi bagatatan.

Mutuwar ita tazo wa wasu mutane kimanin 25 dake tsaka da tafiya akan hanyar su ta Hadeja-Potiskum, dake cikin ƙaramar hukumar Gamawan Jihar Bauchi.

Duk dai a cikin mummunan hatsarin, wasu daga cikin mahayan kimanin guda 10 sun samu munanan raunuka a cikin motar dake tsaka da zabga gudu.

Lamarin maras daɗin ji da gani ya faru ne ranar Alhamis, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

Kwamandan rundunar kare haɗurra ta ƙasa sashin jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Jaridar Punch a safiyar yau juma’a.

Jami’in yace, a cikin mutanen 35 akwai maza 19, mata 11, yara maza guda 2 da kuma yara mata guda uku.

Da jami’in yake zayyana yadda haɗarin ya faru, yace, direban motan da tayi haɗari, ya rasa yadda zai sarrafa motar ne, wanda hakan yasa ya aukawa wasu mutane 11 dake hutawa a ƙarƙashin wata bishiya dake kusa da wajen wankin mota.

Ga yadda Abdullahi, ya zayyana lamarin:

“Kwarai kuwa, an samu mummunan hatsarin mota a Udubo, akan hanyar Hadeja-Potiskum ta zuwa ƙaramar hukumar Gamawa dake jihar Bauchi. Hatsarin ya faru jiya Alhamis, watau 23rd ga watan Maris na 2023.” inji shi.

“Hatsarin ya haɗa da wata motar haya samfurin Toyota Hummer Bus mai lamba ‘JMA 59XA’.”,

“Hatsarin ya faru ne saboda taƙe motar da akayi da kaya masu yawa, gudun wuce sa’a, da yasa tayar motar ta fashe har motar ta ƙasa sarrafuwa.” Inji shi.

Jami’in ya tabbatar da cewa, sun isa wajen ne bayan samun sanarwar faruwar lamarin, inda basui wata wata ba, suka tura jami’an su na ujula domin basu tallafin gaggawa.

Koda suka isa asibiti da masu hatsarin ne aka tabbatar da cewar, mutane 25 sun sheka barzahu yayin da 10 ke ci gaba da amsar magani sakamakon mummunan ciwo da suka ji a jikkunan su.

Gawarwakin wanda suka mutu an ajiye su a dakin ajiye gawa na FMC, Azare.

Daga ƙarshe, bayan jimamin lamarin, jami’in yayi kira ga matuƙa dasu kula sosai wajen bin dokokin tuki, domin rage haɗurra dake sawa a rasa rai da kuma sawa aji ciwo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here