Bincike ya Gano Yadda Ake Cin Zarafin ‘Yan ƙwallon ƙafa mata a Amurka
Wani bincike da aka shafe shekaru ana gudanarwa kan zarge-zargen cin zarafi da rashin nuna ɗa’a a manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na mata a Amurka, ya tabbatar da cewa matsalar ta zama ruwan dare.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Amurka ce ta samar da kwamitin binciken sakamakon zarge-zargen da mata ƴan wasa suka shigar.
Read Also:
Kwamitin ya gano cewa an mayar da cin zarafi da lalata a matsayin ba komai ba, matsalar ta yaɗu kuma tana shafar ƙungiyoyi da dama da ƴan wasa da kuma masu horarwa.
A shekarar da ta gabata ne masu horarwa a rabin manyan ƙungiyoyin mata na Amurka suka yi murabus, yayin da ƴan wasan suka gabatar da zarge-zargen cin zarafin.
Shugabar hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Cindy Parlow Cone, ta bayyana sakamakon binciken a matsayin babban abin damuwa.