Satar Wayar Android: Matasa Sun Cinna wa ɓarawo Wuta

 

Wani ɓarawo ya gamu da ajalin sa bayan wasu matasa sun cinna masa wuta a Cross River.

Ana zargin matashin mai ƙananan shekaru da laifin satar wayar salula ta Android ya arce da ita.

Jami’an ƴan sanda sun yi tofin Allah tsine kan yadda matasan suka ɗauki doka a hannunsu wajen hukunta ɓarawon.

Jihar Cross River- Wasu matasa sun yi wa wani matashi mai shekara 22, taron dangi inda suka cinna masa wuta bisa zargin satar wayar Android a unguwar Atimbo, cikin ƙaramar hukumar Calabar Municipal a jihar Cross River.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa wani ganau ba jiyau wanda ya bayyana yadda lamarin ya auku, ya ce matashin mai suna Eyo riƙaƙƙen ɓarawo ne a yankin sannan an sha jan kunnen sa kan ya daina sata.

Ganau ɗin wanda ya nemi da a sakaya sunan sa, ya ce Eyo ya tafka satar ne a ranar Asabar, inda yayi ɓata dabo ba a sake jin ɗuriyarsa ba har sai ranar Lahadi.

A kalamansa:

“Na san Eyo tun muna makarantar sakandire, ya saba da sata, akwai lokacin da ya sace kusan rabin kuɗin makarantar ƴan ajin mu.”

“Yayin da muke ƙara girma sai Eyo ya cigaba da zama riƙaƙƙen ɓarawo, satar sa ta ƙara munana, an sha kama shi sau da dama, wannan ba shi bane karon farko da aka taɓa yi masa taron dangi ba, yau dai kawai ya haɗu da ajalin sa.”

“Sun fara dukan shi da adda kafin su cinna masa wuta. Abin mamaki shine ba sayar Android kawai yayi ba.”

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da aukuwar lamarin Kakakin hukumuar ƴan sandan jihar, Irene Ugbo, ta tabbatar da aukuwar lamarin sannan tayi Allah wadai da abinda matasan suka aikata.

A yayin da take nuni da cewa ya saɓa doka mutane su ɗauki hukunci a hannun su, ta ce abinda yakamata ayi shine a miƙa wanda ake zargin zuwa ofishin ƴan sandan da ke a unguwar, cewar rahoton Vanguard

“Halaka shi ta wannan mummunar hanyar, ba wai kawai jahilci bane, ya saɓawa doka sannan bai dace ba.” A cewar ta

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here