Bayan Garkuwa da Mutane 85: ‘Yan Bindiga Sun Sassauta Kudin Fansa

 

Ƴan bindigan da suka sace mutum 85 a jihar Zamfara sun sassauta kan kuɗin fansan da suka nemi a ba su.

Ƴan bindigan sun ce yanzu kowane mutum ɗaya dole ne a biya masa N20,000 kafin ya shaki iskar ƴanci.

Sai dai sun kuma gindaya wasu sharuɗɗan waɗanda dole sai an cika su kafin su sako mutanen da suka sace.

Jihar Zamfara- Ƴan bindigan da suka sace mutum 85 a ƙauyen Wanzamai, cikin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara sun amince su karɓi N20,000 a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum ɗaya da suka sace.

Ƴan bindigan sun kuma nemi hukumomi da su janye sojojin da aka kai zuwa cikin ƙauyen a cikin sharuɗɗan da suka gindiya domin sakin mutanen da suka sace, cewar rahoton Punch.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa a ranar Alhamis da ta gabata, ƴan bindigan suka sace kusan kimanin mutum 100 yankin.

Sun bayyana sharuɗɗan su Sun bayar da wa’adin ƙarfe 12:00 na daren ranar Lahadi, inda suka yi barazanar halaka duk wani wanda ba a biya masa kuɗin fansarsa ba kafin cikar wa’adin da suka bada.

Sun kuma yi barazanar cewa idan dai har ba a janye jami’an sojojin da aka jibge a ƙauyen Wanzamai ba, za su cigaba da sace mutanen ƙauyen.

Wani mazaunin ƙauyen, Abubakar Na’Allah ya gayawa majiyar mu ta wayar tarho cewa ƴan bindiga sun turo saƙo cewa N20,000 kawai za su ƙarba kan kowane mutum ɗaya da suka sace a matsayin kuɗin fansa, duba da cewa talakawa ne marasa ƙarfi.

A cewarsa:

“Da farko ƴan bindigan sun nemi da a basu N50m domin sakin mutum 85 ɗin da suka sace waɗanda mafi yawa daga cikinsu mata ne da ƙananan yara da suka shiga daji samo makamashi a ranar Juma’ar da ta wuce.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here