Ministan Lafiya ya Bayyana Yadda Cutar Zazzabin Cizon Sauro ke Kashe ‘Yan Najeriya a Kowane Minti 60

 

Ministan Lafiya, Osagie Ohanire, ya bayyana cewa yan Najeriya 9 na rasa ransu a kowane minti 60 saboda.

Malaria Ministan ya koka kan yadda mutane suke mutuwa a faɗin kasa yayin wata ziyara da ma’ikatar lafiya ta kai.

Ogun Ohanire ya ƙara cewa Najeriya ce gaba-gaba a kamuwa da zazzaɓin cizon sauro a faɗin duniya.

Ogun – Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, ya koka kan yadda ake samun karuwar mace-mace da ciwon dake da alaƙa da zazzabin cizon sauro a faɗin kasar nan.

Dailytrust ta ruwaito ministan ya kara da cewa yan Najeriya 9 ne suke mutuwa da ciwon a kowace awa ɗaya.

Ehanire ya bayyana hakane ranar Litinin a Abeokuta, yayin da tawagar ma’aikatar lafiya da kuma kungiyar taimakon lafiya (SFH) suka ziyarci mataimakiyar gwamnan Ogun, Mrs. Noimot Salako-Oyedele.

Menene dalilin wannan ziyara?

Tawagar ma’aikatar lafiya da kungiyar SFH sun ziyarci mataimakiyar gwamnan ne domin neman goyon bayan gwamnati kan yaki da cutar zazzabin cizon sauro.

Ehanire wanda ya samu wakilcin Timi Obot, ya koka kan cewa a duk mutum hudu da suka kamu da Malaria a duniya ɗaya ɗan Najeriya ne.

Ministan yace:

“Ya zama wajibi mu tashi tsaye domin magance yawaitar kisan da cutar Malaria take yi a faɗin ƙasar nan.”

“Gwamnatin tarayya tare da haɗin guiwar SFH da shirin yaki da cutar Malaria ta ƙasa (NIMET) zasu raba ragar sauro miliyan 3.7m ga magidanta a faɗin kananan hukumomi 20 dake faɗin jahar.”

Najeriya ce gaba-gaba a yawan Malaria a duniya

Da yake tsokaci kan rahoton duniya na 2010, Ministan yace Najeriya ce gaba-gaba inda take da kashi 27 na masu ɗauke da Malaria da kashi 23 da waɗanda suke mutuwa.

A jawabinta, mataimakiyar gwamnan tace gwamnati zata bada dukkanin goyon bayan da ake bukata don kammala rarraba ragar sauron cikin nasara.

Ta kara da cewa ragar tana taimkawa mutane matuka wajen rage kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da wasu cututtuka.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here