CNG ta yi Allah-Wadai da Yadda ‘Yan Bindiga ke Yawaita kai Hare-Hare a Arewacin Najeriya

 

Gamayyar ƙungiyoyin farar-hula a arewacin Najeriya CNG ta yi Allah-wadai da yadda ƴan bindiga ke yawaita kai hare-hare, musamman a yankin, tana zargin gwamnati da gazawa wajen kare rayuka da dukiyar al`umma.

Mahukunta a ƙasar dai suna jaddada cewa jami`na tsaro na bakin koƙarinsu wajen daƙile maharan.

Amma kungiyar ta ce ba ta gani a kasa ba, kuma wannan ne yasa ta shirya wani taro da nufin hada al`ummomin yankin domin samar wa kai mafita, kamar yadda Alhaji Nastura Ashiru shugaban kwamitin amintattuna kungiyar, ya shaida wa BBC.

“Ya kamata duk wanda yake ƙoƙonta a da ya cire a yanzu cewar gwamnatin nan ta kasa gudanar da aikin da ya kamata na tsare rayuka da dukiya da mutuncin ƴan ƙasa” in ji shi.

Ya ƙara da cewa “hare-hare a hanyar Kaduna zuwa Abuja da yadda ƴan bindiga suka addabi yankin Shinkafi da sabon Birni ya isa ya nuna cewa gwamnati ta gaza ba za ta iya ba.”

A sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar da ke jajantawa mutanen Sokoto bayan harin ƴan bindiga da suka ƙona matafiya da dama, Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa yana mai cewa “jami’an tsaro za su ci gaba da koƙari na kawo ƙarshen waɗannan miyagun mutane”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here