An Kuma: ‘Yan Bindiga Sun Sace Limami da Masallata 10 a Sokoto
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun sake kai hari a Sokoto a kauyen Gatawa inda suka sace babban limami, Aminu Garba, da wasu masallata 10
Hakan dai yana zuwa ne bayan mummunan harin da ‘yan bindigan suka kai wa matafiya a jahar ta Sokoto suka hallaka da dama ta hanyar kona su da ransu
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ya ce zai tuntubi jami’in da ke kula da yankin kafin ya yi tsokaci kan lamari.
Sokoto – ‘Yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma’a a jam’i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jahar Sokoto.
An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma’a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai
Dan Majalisa, Sa’idu Ibrahim ya tabbatar da faruwar da harin.
Dan majalisar jahar mai wakiltar mazabar Sabon Birni na Kudu, Sa’idu Ibrahim, ya tabbatar da harin, ya ce mutane ukun da suka jikkata suna karbar magani a babban asibitin Wamakk.
Ya ce wata mata, wacce aka harba a kauyen Dama, ta rasa kafar ta yayin da likitoci suka datse saboda an kasa gyara kafar.
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan jahar Sokoto, ASP Sanusi Abubakar, ya ce zai tuntubi jami’in da ke kula da yankin sannan ya bada bayani, amma bai bada bayanin ba har lokacin hada wannan rahoton.
Tunda farko, SaharaReporters ta ruwaito cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta fatattaki yan bindiga daga kasa.
Buhari ya bada wannan tabbacin ne a ranar Juma’a a yayin da tawagar Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kai wa Gwamna Aminu Tambuwal ziyarar ta’aziyya game da kashe matafiya 23 da yan bindiga suka yi.