Yaduwar Korona: Shugaba Buhari ya Saka Sabuwar Doka
Najeriya ta kafa sabuwar dokar hukunta masu saba dokokin da aka kafa don dakile yaduwar COVID-19.
A ranar Talata, mutane 15 suka rasa rayukansu sakamakon cutar.
Adadin wadanda suka kamu da cutar a duniya ta zarce milyan 100.
Shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan sabon dokan daurin watanni 6 a gidan kaso kan duk wanda aka kama yana saba dokokin kariya daga cutar Korona.
Read Also:
Shugaban kasan ya rattafa hannunsa dokar a Abuja, ranar Laraba.
Kamar yadda dokar killata, sashe 34 na sabon dokan ya tanada, duk wanda ya saba, za’a ci shi tara ko kuma yayi watanni shida a Kurkuku.
Me dokar ta kunsa?
“Dokar ta kunshi baiwa juna tazara a dukkan taruka, yayinda dukkan wadanda zasu kasance a wajen su sanya takunkumin rufe fuska, su wanke hannayensu, kuma a duba zafin jikinsu kafin su shiga.
Hakazalika dokar ta tanadi kada a samu mutane sama da 50 a waje guda, illa wuraren Ibada.”