Corona: Bisa Kuskure ne Kwayar Cutar ta Fita Daga ɗakin Gwaji a China – Dr Robert
Read Also:
Tsohon darektan hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Amurka, ya faɗa wa kwamitin bincike na majalisar dokokin kasar cewa ya yi ammanar cewa bisa kuskure ne kwayar cutar korona ta fita daga dakin gwaji a kasar China.
Dakta Robert Redfield, wanda ya jagoranci hukumar ta CDC daga 2018 zuwa 2021 ya bayyana haka ne a rana ta farko ta sauraran bahasin jama’a na kwamitin majalisar wakilai da aka dorawa alhakin gudanar da bincike a kan asalin cutar ta korona.
Ya ce a nazarin farko da na yi, na yi amanar cewa kuma har yanzu ra’ayi na bai sauya ba, a kan cewa bisa kuskure ne kwayar cutar korona ta fita daga dakin kimiya , ba haka ne kawai ta bulla ba.
Ra’ayinsa ya zo ɗaya da na shugaban hukumar bincike na FBI, Christopher Wray wanda a hirar da ya yi a baya bayanan ya bayyana cewa hukumarsa ita ma tayi irin wannan nazari na dan lokaci.
Sai dai China ta musanta zargin.