Bincike ya Nuna Cewa Cutar Corona ta fi Nace wa Tsofaffin Mata
Wani bincike da masana suka yi a jami’ar Glasgow da ke Scotland ya nuna cewa cutar corona ta fi nace wa mata da suke da yawan shekaru.
Kuma a cewar binciken hakan ya fi faruwa ne a yankuna da ba su da abubuwan more rayuwa yadda ya kamata.
Read Also:
Haka nan kuma cutar ta corona ta fi nace wa mutane waɗanda suka kasance suna da wasu cututtukan tun asali, kamar na raunin hankali, da lalurar da ke shafar hanyoyin numfashi, ko kuma cutar damuwa mai tsanani.
Wata mata mai suna Jayne Gemwell mai shekara 55 da ke zaune a wani kauye na Scotland ta kamu da corona tun cikin watan Maris na shekara ta 2020, amma har yanzu ba ta warware gaba ɗaya ba duk da dai ta koma aiki.
Ta yi fama da wahala wurin lumfashi, a cewarta “A rana ta biyu bayan kamuwa da cutar na ji kamar an ɗora min giwa ne a kan ƙirjina.”