Gwamnan Cross Rivers ya Sanya Dokar Kulle a ƙauyuka Huɗu da ke Jihar

 

Gwamnan jihar Cross Rivers ya sanya dokar kulle a wasu ƙauyuka huɗu na ƙaramar hukumar Yaba ta jihar.

Gwamna Bassey Otu ya sanya dokar kullen ne biyo bayan rikicin da y ɓarke kan filaye da iyakoki a ƙauyukan.

Kakakin gwamna Otu shi ne ya sanar da sanya dokar kullen a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Satumba.

Jihar Cross Rivers – Gwamna Bassey Otu na jihar Cross Rivers a ranar Talata ya sanya dokar kulle a ƙauyukan Ugaga, Igbekurekor, Benekaba da Ijama na ƙaramar hukumar Yala ta jihar.

Gwamnan ya sanya dokar kullen ne bayan an samu ɓarkewar rikici a ƙauyukan, cewar rahoton PM News.

Rikicin filaye da iyakoki a tsakanin ƙauyukan guda huɗu ya jawo matsalar rashin tsaro a yankin wacce ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

A cewar gwamnan, an sanya dokar kullen ne domin hana cigaba da aukuwar rikicin da kuma ba jami’an tsaro damar shawo kan matsalar.

Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamna Otu, Mista Emmanuel Emmanuel Ogbeche, ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, a birnin Calabar, babban birnin jihar.

Dalilin gwamna Otu na sanya dokar kullen Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“Dokar kullen ta zama wajibi biyo bayan rikicin kan iyaka da ke haifar da barazanar tsaro wacce ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyin jama’a”

“Don haka na sanya dokar kulle a ƙauyukan Ugaga da Igbekurekor na ƙaramar hukumar Yaba, da ƙauyukan Benekaba da Ujama.”

Otu ya umarci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da ta samar da shirin gaggawa na kayan agaji ga mutanen da rikicin ya ritsa da su, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Gwamnan ya ja kunnen sarakunan gargajiya Ya buƙaci sarakunan gargajiya na ƙauyukan da su gaggauta samar da hanyoyin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Gwamnan ya bayyana cewa zai ɗora musu alhakin duk wani rashin bin doka da oda da ya sake aukuwa a yankunansu.

Ya kuma buƙaci al’ummar ƙauyukan da abin ya shafa da su haƙura da rikicin su zauna lafiya da junansu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com