Mambobin ƙungiyar NURTW Sun Dambatu a Abuja

 

Mutanen birnin tarayya Abuja sun shiga firgici a ranar Talata lokacin da mambobin NURTW suka yi rikici inda har bindigu aka harba.

Shaidar ganau ba jiyau ba ya bayyana cewa ba zai iya tantance cewa ko bindigun da aka harba daga ƴan sandan ne ko daga mambobin ƙungiyar ba.

An fahimci cewa rikicin ya auku ne a tsakanin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Tajudeen Baruwa da magoya bayan Badru Agbede.

FCT, Abuja – An shiga tashin hankali da firgici a birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, lokacin da tsagin ƙungiyar direbobin motocin sufuri ta ƙasa (NURTW) suka ba hammata iska.

Shaidar ganau ba jiyau ya tabbatar da cewa an yi harbe-harben bindiga a lokacin rikicin, cewar rahoton Channels tv.

Shaidar gani da ido ya magantu kan rikicin NURTW a Abuja

Da yake magana bayan ya nemi a sakaya sunansa, shaidar gani da idon ya bayyana cewa ba zai iya tabbatar da cewa bindigun da aka harba daga ɓangaren ƴan sanda ne ba, ko mambobin ƙungiyar masu faɗa da juna.

An tattaro cewa rikicin ya auku ne a tsakanin mambobin ƙungiyar da ke biyayya ga shugaban ƙungiyar na ƙasa, Tajudeen Baruwa, da magiya bayan abokin hamayyarsa Badru Agbede, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Baruwa ya sha yin kira ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) da ta sanya baki domin a warware rikicin, ta yadda za a dawo da mambobinsa a hedikwatar ƙungiyar ta ƙasa wacce a yanzu haka take a ƙarƙashin ikon ƴan sanda.

Jami’an ƴan sanda har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba su ce komai ba dangane da rikicin da ya auku.

Abun sani dangane da rikicin NURTW a Abuja Baruwa shi ne tsohon shugaban NURTW a jihar Ogun, yayin da Agbede ya riƙe muƙamin shugabancin ƙungiyar a jihar Legas Kafin a zaɓe shi a karo na biyu, Baruwa ya samu saɓani da reshen ƙungiƴar na jihar Legas a ƙarƙashin shugabancin Musiliu Akinsanya wanda aka fi sani da MC Oluomo, inda suka fice daga ƙungiyar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com