Gwamnoni 4 da Kotu ba za ta ƙwace Nasararsu ba – Fasto Elijah Ayodele

 

Fasto Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya bayyana cewa wasu gwamnonin kotu ba za ta ƙwace nasararsu ba.

Babban faston a wani rubutu da ya yi a Twitter, ya lissafo gwamnoni huɗu na jam’iyyun PDP, APC da Labour Party.

Idan za a tuna dai kotunan zaɓe a jihohi 25 masu sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna sun tanadi hukuncinsu wanda za su zartar a ƙarshen watan Satumba.

Jihar Legas – Fasto Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya yi hasashen cewa ba kotun zaɓen da za ta soke zaɓen gwamnoni huɗu a Najeriya.

Jerin sunayen gwamnonin da Ayodele ya hango sun haɗa da na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), All Progressives Congress (APC) da Labour Party.

A cewar The Punch, kotunan da ke zama a jihohi 25 cikin 28 da aka gudanar da zaɓen gwamna na ranar 18 ga watan Maris, ka iya yanke hukuncinsu kafin ƙarshen watan Satumba, domin da yawa daga cikinsu sun tanadi hukuncinsu.

Amma a cikin sabon hasashen da ya fitar a Twitter, Ayodele ya bayyana cewa babu kotun da za ta soke zaɓen gwamnoni huɗu, duk kuwa da irin abubuwan da abokan takararsu suka bayyana a gaban kotu.

Ayodele ya yi hasashen makomar Kefas, Sanwo-Olu, Oti, Mbah, da Eno

A cewar babban faston kotu ba za ta iya ƙwace nasarar Agbu Kefas, gwamnan PDP na jihar Taraba, Alex Otti na jam’iyyar Labour Party a jihar Abia.

Fasto Ayodele ya kuma bayyana cewa da wuya a iya ƙwace nasarar gwamnan jihar Enugu na jam’iyyar PDP, Peter Mbah, idan gwamnan ya koma ga ubangiji.

Babban malamin addinin ya kuma ƙara da cewa bai ga wanda zai ƙwace nasarar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu na jam’iyyar APC ba, duk kuwa da irin abin da masu shigar da ƙara suka gabatar a kotu.

Ayodele ya kuma bayyana cewa kotu ba za ta soke zaɓen gwamnan PDP Umo Eno na jihar Akwa Ibom ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com