Na Daina Jin Dadin Rayuwa, Burina na Cika da Imani – Aminu Dantata

 

 

Fitaccen attajiri kuma jigon Arewa, Dantata ya ce babu abin da ya rage masa na jin dadin duniya a yanzu.

Dantata ya ce yana neman kowa ya yafe masa, kuma shi ya yafewa duk wanda ya taba yi masa ba daidai ba.

Kashim Shettima ya kai wata ziyara gidan Dantata, sun tattauna kan batutuwan da suka shafi Najeriya.

Jihar Kano – Jigo dattijon kasa kuma fitaccen dan kasuwa, Aminu Alhassan Dantata ya ce a yanzu dai ya daina jin dadin rayuwa, burinsa kawai ya cika da imani, Daily Trust ta ruwaito.

Dantata mai shekaru 91 ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin abokin takarar Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023 a APC, Kashim Shettima.

Ya bayyana cewa, daga yarinta zuwa yanzu, ya samu damar haduwa da mutane da yawa a fadin kasar nan, kuma ya kulla abota da yawa, amma yanzu dakyar ya iya kirga 10 da suka rage a raye.

A kalamansa:

“Na taka dukkan jihohin Najeriya kuma na yi abubuwa tare da mutane a dukkan jihohin, da yawa abokai na ne amma abin takaici, dukkan mutanen da na sani, da wahala na kirga 10 da suka rage a raye.”

“Magana ta gaskiya, a yadda nake yanzu, ina jiran wa’adina ne kawai. Na daina jin dadin rayuwa. Ina fatan cikawa ne da imani kawai. “Ina fatan ban sabawa kowa ba a rayuwa.

Idan na sabawa wani, ina fatan su tausaya su yafe mani. Idan wani ya saba mani, na yafe masa.

“Ni kadai ne na saura a cikin ahali na da ke raye tare da jikoki.”

Na ji dadin ziyara, Allah ya daidaita Najeriya, inji Dantata Yayin da yake bayyana jin dadi da yaba wannan ziyara ta Shettima, Dantata ya yiwa Najeriya addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A cewarsa:

“Ya Allah kada ya barmu da iyawarmu mu kadai, muna rokonsa da ya ci gaba da shiryar damu da kare mu.”

Manufar ziyara zuwa jihar Kano

A tun farko, Shettima ya ce ya je jihar Kano ne domin ci gaba da tallata manufar gangamin siyasarsa tare da Bola Tinubu gabanin zaben 2023, haka nan Platinum Post ta tattaro.

Ya yi wannan ziyara ne tare da gwamnan Kano mai ci, Dr Abdullahi Umar Ganduje, Musa Gwadabe, Janar Lawal Jafaru da Tanko Yakasai

Hakazalika, ya kai ziyara zuwa cibiyar aikin yaki da cutar daji ta jihar Kano, wacce ake dab da kammalawa kafin daga bisani ya zarce zuwa filin jirgin sama.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here