Ministan Kwadago, Ngige ya yi Alkawarin Kara Albashin Ma’aikata a 2023
Chris Ngige ya yi zama da Mai girma Muhammadu Buhari a Aso Rock a kan abin da ya shafi albashi.
Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasa ya ce gwamnatin tarayya na kokarin yin karin kudi.
Tsadar rayuwa da yawan tashin farashin kaya a kasuwa suka jawo karin zai zama dole a 2023.
Abuja – Gwamnatin tarayya ta ce ba da dadewa ba za ta sanar da karin albashin da aka yi wa ma’aikata da jami’an gwamnati saboda halin da ake ciki.
The Nation ta rahoto Ministan kwadago da samar da ayyuka, Chris Ngige ya ce wani kwamiti a kan albashi yana duba abin da ake biyan ma’aikatan kasar.
Dr. Chris Ngige ya yi wannan bayani ne bayan ya yi wani zama a bayan labule da Mai girma Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a ranar Talata.
Yawan tashin farashin kaya a kasar ne ya jawo kwamitin ya zauna a kan maganar karin albashi.
Ministan ya yi alkawarin albashin ma’aikata zai karu.
Kwamitin shugaban kasa yana zama da RMFAC
“Kwamitin shugaban kasa a kan albashi yana aiki tare da hukumar yanka albashin ma’aikata na kasa. Hukumar ne ke da alhakin yanke albashin ma’aikata.
Read Also:
Idan ku na aiki a ma’aikatun kasuwa kuma ku na neman taimako, za su taimaka maku. Su na da tsarin abin da ya kamata a rika biyan duk wani ma’aikaci.
Saboda haka su na aiki da kwamitin shugaban kasa wanda Ministar kudi ta ke jagoranta, ni ne dayan shugaban kwamitin da yake duba bukatun ma’aikatan nan.”
– Chris Ngige
Shekarar rigima da ‘yan kwadago Punch ta rahoto Ministan kwadagon yana nunawa manema labarai cewa yayin da za a shiga sabuwar shekara, gwamnati za tayi kokarin ganin an kara albashi.
Batun hakkokin ‘yan kwadago da matsalar rashin ayyukan yi da kuma sabani da ma’aikata a Najeriya, yana cikin abin da ya sa Ngige ya gana da shugaban kasa.
A tattaunawar da aka yi da shi, rahoto ya zo cewa Ministan ya yi magana a kan rikicin gwamnatin tarayya da ‘Yan ASUU da sauran kungiyoyin da ke jami’oi.
A game da batun albashin watanni takwas na ma’aikatan jami’o’in gwamnati da aka ki biya, Ngige ya ce sun bukaci kotu ta raba gardama tsakaninsu da ma’aikatan.
Mai girma Ministan ya ce ana sa rai da kudin da gwamnati take da shi, za a iya yin wani hobbasa wajen ganin albashin sauran ma’aikata ya karu a shekarar badi.
Likitoci na neman karin kudi
An rahoto wani jagoran NARD, Dr. Emeka Innocent Orji yace an shafe sama da shekaru 10 rabon da gwamnatin tarayya ta karawa Likitoci albashi a Najeriya.
Dr. Emeka Innocent Orji ya nuna a duk wata a Duniya, alkaluma sun nuna kasashen waje suna karbe Likitoci 160 daga kasar nan, kimanin Likita shida a duk rana.