Dakarun Fadar Shugaban Kasa Sun Damke Manyan ‘Yan Ta’adda 8
Hedkwatar Tsaro ta Najeriya tace dakarun sojoji sun damke manyan ‘yan ta’adda 8 a babban birnin tarayya na Abuja.
Gagarumin aikin kamar yadda shugaban rundunar ya bayyana, dogaran fadar shugaban kasa ne suka yi shi a Deidei Abbatoir da kauyen Dukpa daka Gwagwalada.
An yi wannan aiki ne kasa da watanni biyu bayan sojojin fadar shugaban kasa 8 sun halaka a wani farmaki da ‘yan ta’adda suka kai musu.
FCT, Abuja – Rundunar sojin Najeriya ta kai samame maboyar ‘yan ta’adda inda suka cafke manyan ‘yan ta’adda takwas a yankin.
Read Also:
Hedkwatar tsaro ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Augustan 2022 inda ta kara da cewa an kama ‘yan ta’addan ne a maboyarsu dake Deidei Abbatoir da kauyen Dukpa a karamar hukumar Gwagwalada, The Nation ta rahoto.
Dakarun fadar shugaban kasan ne suka aiwatar da aikin. Idan za a tuna, hafsoshin soji biyu da sojoji shida daga cikin dogaran fadar shugaban kasan sun rasa rayukansu sakamakon harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai yankin Bwari.
An gano cewa a sansanin ne ‘yan Boko Haram da mambobin ISWAP ke kafa dandalinsu.
Kamar yadda daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana, an kai samamen a ranar 13 ga watan Augusta.
“A samamen, mutum takwas aka kama da zargin ta’addanci, bindigu kirar AK47 guda biyar da wasu guda uku aka samu.”