Jami’an Tsaro Sun Dakile Yunƙurin Sace Taragon Jirgin ƙasa a Maiduguri
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno ta ce ta kama wasu mutane da suka yi yunƙurin sace tarago-tarago na jiragen ƙasa daga tashar jirgin da ke birnin Maiduguri.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mohammed Yunus Lawan, ya ce an kira su daga tashar jirgin kuma aka shaida musu cewa an ga wata babbar mota na shirin kwashe tarago-taragon, inda jami’ansu suka isa cikin gaggawa.
Read Also:
“Kayan sun haɗa da taragon jirgi uku, kuma a nan take muka kama wani mutum mai suna Aliyu Mainasara,” kamar yadda kwamishinan ya faɗa wa gidan talabijin na NTA.
“Wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa shugaban hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa na Najeriya ne ya ba shi umarnin kwashe taragon zuwa jihar Filato saboda gwamnatin jihar za ta ƙirƙiri layin dogo a cikin birnin Jos.”
Sai dai kwamishinan ya ce mutumin bai nuna wata shaida da za ta tabbatar da iƙirarin nasa ba.
Wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya na cewa mutum shida ‘yan sandan suka kama da zargin sace tarago-taragon.