Dakarun Sojojin Najeriya Sun Ceto Mutane 6 da aka yi Garkuwa da su a Jihar Kaduna

 

Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar rage mugun iri ta hanyar sheƙe wani ɗan bindiga a jihar Kaduna.

Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ceto wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.

Jajirtattun dakarun sojojin sun kuma samu nasarar ƙwato muggan makamai a hannun ƴan bindigan tare da raunata da dama daga cikinsu.

Jihar Kaduna – Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su tare da kashe wani ɗan bindiga ɗaya a jihar Kaduna, cewar rahoton The Nation.

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na sojoji runduna ta daya ta Sojojin Najeriya, Laftanal-Kanal Musa Yahaya wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce an ceto mutanen ne a ranar Juma’a, 13 ga watan Oktoba.

Yahaya ya ce cigaba da aikin kakkaɓe ƴan bindiga da dakarun rundunar ke yi, na cigaba da samun sakamako mai kyau, rahoton Vanguard ya tabbatar.

A kalamansa:

“Rundunar ta yi aiki da sahihan bayanan da ta samu kan sace mutum shida da aka yi a Hayin Tsando a yankin Maraban Jos, a ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.”

“Dakarun sojojin sun yi gaggawar yin shiri, suka fara aikin bincike da ceto. Sojojin sun yi arangama da ƴan ta’addan da kuma masu aikata laifuka kuma an yi musayar wuta mai tsanani.”

“A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutum shida da aka yi garkuwa da su, sun ƙwace bindigu ƙirar AK 47 guda biyu tare da kashe ɗan bindiga guda ɗaya yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.”

Yahaya ya kuma bukace su da su ci gaba da kai hare-hare har sai an kawar da duk wasu masu aikata laifuka a sashin gaba ɗaya.

Ya kuma yi kira ga ma’aikatan lafiya da su riƙa lura da waɗanda suka samu raunukan harbin bindiga, sannan su kai rahoto ga rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com