Jami’an Tsaro Sun Kama Matashin da Ake Zargi da Satar Buhun Shinkafa 47

 

Jami’an yan sanda a jihar Ogun sun cika hannu da wani matashi dan shekaru 25.

Ana zargin Damilola Bada da wawure buhun shinkafa 47 mallakin uwar dakinsa wanda farashinsu ya kai miliyan 2.5.

Mai kamfanin Chicken & Co Company ta gano badakalar da aka tafka ne a yayin bincike.

Jihar Ogun – Rundunar yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum kan zargin satar buhun shinkafa 47 mallakin uwar dakinsa a yankin Ijebu da ke jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Omolola Odutola, ta gabatarwa manema labarai a ranar Asabar, 14 ga watan Oktoba, jaridar Punch ta rahoto.

Yadda aka kama matashi kan zargin satar buhun shinkafa 47

Wanda ake zargin Damilola Bada, ya sace buhun shinkafa mallakin wani kamfani, Chicken & Co., wanda farashinsa ya kai N2,500,000.

A cewar Odutola, mai kamfanin, Oluremi Olabode, ta yi karar lamarin satar kayayyakin da aka yi mata a ofishin Igbeba da ke jihar Ogun wanda ya yi sanadiyar kama Bada mai shekaru 25, rahoton Peoples Gazatte.

Jawabin ya ce:

“A ranar 13 ga watan Oktoban 2023 wata Oluremi Olabode, “mace” mai kamfanin Chicken & Co Company, ta kai karar sata, wanda wani mai kula da shagon ajiyanta mai suna Damilola Bada mai shekaru 25 ke da hannu a ciki.

“Ta zargi Damilola da hada kai da dauran ma’aikata don sace buhun shinkafa arba’in da bakwai, wanda ya kai miliyan biyu da dubu dari biyar.

“Bayan binciken wajen ajiyan, sai mai karar, Oluremi Olabode ta gano satar da aka tafka. Sakamakon haka, DPO na Igbeba ya kama Damilola Bada sannan aka yi masa tambayoyi. Yayin tambayoyin, Damilola ya gaza bayar da gamsasshen bayani game da batan buhun shinkafar da ke karkashin kulawarsa.”

Ta yi kira ga al’umma da su sanya idanu sosai sannan su kai karar duk wasu abubuwa da basu gamsu da shi ba garinsu ga ofishin yan sanda mafi kusa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com