Mun Daƙile Yunƙurin Kutse ta Intanet Har Sau Miliyan 13 Lokacin Zaɓe – Kashifu Inuwa

 

Hukumomi a Najeriya sun ce ƙasar ta daƙile yunƙurin kutse ko hare-hare a kan hanyoyin sadarwa na intanet har kimanin miliyan 13 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

Babban daraktan hukumar bunƙasa fasahar sadarwa ta Najeriya, wato NITDA, Kashifu Inuwa AbdulLahi, shi ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da BBC, inda ya ce an samu nasarar ce sakamakon wasu cibiyoyi da aka kafa don yaƙi da kutsen ta intanet da kuma wani kwamiti na musamman da aka kafa da ya ƙunshi hukumomin NITDA da NCC da Galaxy Backbone.

Ya ce a ranar zaɓe kaɗai sun daƙile yunƙurin kutse har miliyan shida da dubu ɗari tara.

Daraktan na NITDA ya ce an yi ƙoƙarin yin kutsen daga cikin gida da kuma ƙasashen waje saboda suna amfani da wasu manhajoji.

Ya ce kutsen ya shafi shafukan intanet na hukumomi da na kamfanoni masu zaman kansu da kuma na hukumar zaɓe wanda shi ne aka fi kai wa hari saboda zaɓe.

Ya ce babban hatsari da ke tattare da yin kutsen, shi ne hakan zai sa a deɓi bayanai da canza wasu da kuma sanya wa mutane shakku kan amincewa da sahihan bayanai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here