Satar Daliban Kagara: Hukumar Sojojin Najeriya Ta Tura Jami’anta Su Nemo Masu Garkuwar
Hukumar Sojoji ta saki jawabinta na farko kan sace dalibai makarantar sakandare a Kagara.
Wannan ya biyo bayan jawabin Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi.
Gwamnan Neja ya tabbatar da sace dalibai akalla 27 da Malamai 3.
Hukumar Sojin Najeriya ta ce ta tura jami’anta neman masu garkuwa da mutanen da suka yi awon gaba da daliban makarantar sakandare GSC Kagara, jahar Neja.
Diraktan hulda da jama’a na hukumar, Birgediya Janar Mohammed Yerima, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Laraba a Abuja.
Read Also:
Yerima ya ce hukumar ta bazama neman yan bindigan domin cetin yaran. Ya ce rahotanni sun nuna cewa yan bindigan sun samu shiga cikin makarantan ne da safiyar Laraba suka sace daliban makaranta da malamansu.
“Hukumar Sojojin Najeriya bisa aikinta na tabbatarwa daukacin yan Najeriya cewa jami’anta tare da wasu jami’an tsaro na kan neman tsagerun da kuma ceto yaran da aka sace,” yace.
“Bayan haka, hukumar Sojin na kira ga jama’a su baiwa hukumomin tsaro kowani labarin da suka samu kan tsagerun.”
Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello, ya tabbatar da cewa an sace dalibai 27, ma’aikata 3, da wasu mutane 12 a cikin makarantan.