Sanadiyyar Tashi da Faduwar Jirgin Sojojin Sama a Abuja

 

An samu bayanai akan jirgin da injinsa ya lalace ya fado daga sama yayi sanadiyyar mutuwar mutane 7.

Dama duk sojojin sama na Najeriya NAF201, ne cikin jirgin suna neman inda ‘yan Kagara da aka sace suke

Suna tsaka da neman ne injin jirgin ya lalace da misalin 10:39am ya fado tantagaryar titin garin Abuja

Ashe sojojin sama na NAF201 da suka yi hatsari a jirgin sama, har mutane 7 da matukan jirgi da suka mutu a Abuja, suna neman wadanda aka sace a Kagara ne, kamar yadda bayanai suka bayyana a ranar Lahadi da yamma.

Kamar yadda aka samu labari, bayan kara wa jirgin mai a Abuja, jirgin ya bazama neman ‘yan makarantan Kagara da aka sace ne a jahar Neja, Vanguard ta wallafa.

“Jirgin ya nufi Abuja don shan mai, injin jirgin ya samu matsala yayin da ya keta hazo ya kasa sakkowa duk da kokarin da yayi don sauka lafiya.”

Labarai sun kammala akan yadda hafsin sojin sama suka rasu a filin jirgin. Muna fatan Ubangiji yayi musu rahama, sun mutu yayin yi wa kasa bauta.

Ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ya sanar da yadda lamarin ya faru inda yace injin jirgin ya lalace ne da misalin 10:39am sannan ya fadi kasa ne a tantagaryar titin filin jirgin sama Abuja Runway 22.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here