Babban Muhimmin Dalilin da ya sa Gwamnatina ta Canza Fasalin Naira Dab da Zaɓen 2023 – Buhari

 

Muhammadu Buhari ya bayyana muhimmin dalilin da ya sa gwamnatinsa ta canza fasalin Naira ana dab da zaɓen 2023.

Tsohon shugaban kasan ya ce ya yi haka ne domin nuna wa yan Najeriya cewa babu hanyar samun mulki cikin sauƙi.

Ya kuma ce gwamnatinsa ta samu nasara gagara misali a ɓangarorin tsaro da kuma tattalin arzikin ƙasa.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al’amuran yau da kullum.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi bayanin manufar sake fasalin Naira da gwamnatinsa ta bullo da shi a lokacin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.

Buhari ya bayyana cewa ya canja fasalin Naira ne domin nuna wa ƴan Najeriya babu hanyar samun mulki cikin sauƙi, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Tsarin sauya kuɗin da babban bankin Najeriya (CBN) ya aiwatar a karkashin gwamnan lokacin, Godwin Emefiele, ‘yan Najeriya da dama na ganin ya haifar da kunci saboda karancin takardun kudi.

A hirar da ya yi ta farko tun bayan barin mulki, wadda aka watsa a daren ranar Litinin a gidan talabijin na Najeriya (NTA), Buhari ya ce:

“Abin da ya sa muka yi haka shi ne domin ƴan Najeriya su gane kuma su amince cewa babu wata hanya mafi sauki wajen hawa kan gadon mulki saboda mulki ba abu ne mai sauƙi ba.”

“Kamar yadda na sha nanatawa na nemi takara sau uku amma duk sai dai na kare a kotun kolin Najeriya.”

‘Yan Najeriya da dama za su ce wannan wauta ce. Sun gwammace su sami hanya mafi sauƙi da sauri wajen hawa mulki, kuma hanyar ita ce su tara kuɗi ta yadda zasu yaudari mutane su cimma burinsu.”

Muhimman wuri biyu da na samu nasara – Buhari

Buhari ya ce manyan nasarorin da ya samu ita ce ta fannin tsaro da tattalin arziki, yana mai cewa a karkashin gwamnatinsa an kwato yankunan da Boko Haram ta kwace a jihar Borno.

Tsohon shugaban kasar, wanda ya ce bai taba daukar sha’anin ‘yan Najeriya da wasa ba, ya ce bai tara kadarorin haram ba tsawon shekaru takwas a kan mulki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com