Bai Kamata Ramsdale ya Rika Zaman Benci a Arsenal ba – David Seaman

 

Aaron Ramsdale yana da gogewa a tsaron raga, bai kamata ya rika zaman benci a Arsenal ba, in ji tsohon golan Gunners, David Seaman.

Ramsdale na takara da David Raya, wanda Arsenal ta dauka aro daga Brentford kafin fara kakar bana.

Koci Mikel Arteta na amfani da dan kasar Sifaniya a Premier League, wanda ya tsare raga a fafatawa takwas, shi kuwa Ramsdale ya yi wasa hudu zuwa yanzu.

Ramsdale mai shekara 25, ya yi zaman benci a karawar da tawagar Ingila ta yi da Arewacin Macedonia ranar Litinin a wasannin neman shiga Euro 2024.

Seaman ya ce ”Idan har ba ya buga wa Arsenal wasanni da yawa, hakan zai shafi makomarsa a tawagar Ingila, wadda ta samu gurbin shiga gasar da Jamus za ta dauki bakunci a badi.

Kocin Ingila, Gareth Southagate ya shaida wa Ramsdale cewar ba zai yi masa alkawarin gurbi a tawagar Ingila ba, wadda za ta buga Euro 2024, idan yana ci gaba da zaman benci.

Ana sa ran Ramsdale zai tsare ragar Arsenal a wasan da za ta fuskanci Brentford a Premier League, Raya ba zai yi wasan ba, ba damar ya fuskanci kungiyarsa da ta bayar da aronsa ga Gunners.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com