Dalilin da Yasa Gwamnatin Jahar Kano ta Dakatar da ni – Abduljabbar Nasir Kabara

 

An bayyana dalilin da yasa Gwamna Abdullahi Ganduje ya haramta wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara yin wa’azi a Kano.

Kabara ya yi zargin cewa hakan ya kasance ne saboda bai taba marawa gwamnan baya ba a zaben gwamna na 2019.

Malamin ya kara da cewa malamai da dama a jahar na aiki tare da gwamnati don adawa da shi Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi magana a kan dalilin da yake ganin shine ya sa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shi daga yin wa’azi.

A tattaunawarsa da jaridar Daily Trust bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya dauki wannan matakin a kansa, Sheikh Kabara ya yi zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa ba wai lamarin addini ba.

Malamin ya ce gwamnan ya bi ta kansa ne saboda ya yi adawa da shi a lokacin zaben gwamna na 2019 a jahar.

“Dalilan a bayyane suke. Mutumin da ya dauki hukuncin (Ganduje) ya fadi lokuta da dama cewa baya yafiya.

“Na yi yaki da shi a lokacin zaben karshe da aka yi kuma ya yi alkawarin ramawa.

Illa kawai ya dauki matakin da bai dace ba a lokacin da bai dace ba.

Don haka wannan haramcin siyasa ce karara, bai da wani alaka da addini.”

Da yake kira ya mabiyansa kan su shirya kuri’unsu don zabe na gaba, Kabara ya ce ainahin makiyansa sune sauran malamai, ba wai gwamnati ba inda ya kara da cewa kawai dai a yanzu jahar na aiki ne a madadinsu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here