Yadda Mutane Shida(6) Suka Rasa Rayukan su a Titin Birnin Gwari

 

 

Rayukan mutane 6 sun salwanta yayin da wasu 6 suka jigata sakamakon mummunan hatsarin da ya auku a titin Birnin Gwari.

‘Yan bindigan da jami’an tsaro suka biyo ne suka haddasa hatsarin bayan sun budewa ababen hawa wuta.

Harsashi ya samu wani direba daga nan motar ta kwace masa inda ta dinga tintsirawa a kan titin kafin ta tsaya Mutane shida sun rasu sakamakon hatsarin da ‘yan bindiga suka haddasa a kan babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Wasu mutum shida daga cikin wadanda suka yi hatsarin sun samu miyagun raunika.

‘Yan bindigan da aka biyo sakamakon sintirin da jami’an tsaro suka tsananta a yankin, sun hau babbar hanyar inda suka dinga harbin ababen hawa da ke wucewa. An harbi daya wani matukin wata motar haya a yayin da suke ruwan wutar, TVC News ta wallafa.

Daga nan ne motar ta kwace masa inda ta dinga juyawa a titi kafin daga bisani ta tsaya.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce ‘yan bindigan sun tsere daga titin.

Gwamnatin jahar Kaduna ta yi alhinin aukuwar lamarin inda ta yi addu’ar rahama ga mamatan tare da fatan samun sauki ga wadanda suka samu rauni.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here