Dalilin da Yasa na Fice Daga Zauren Majalisa Ana Tsaka da Muhawara – Sanata Ndume

 

 

“Babu shakka akwai rashin jituwa da ke faruwa a majalisa tsakanin wanda yake jagorancin da kuma wasu, amma duk lamarin ‘yan kanzagi ne masu shiga tsakani suna zuga,” in ji Sanata Ali Ndume.

Waɗannan kalamai na zuwa ne biyo bayan zargin cewa babban mai tsawatarwa na majalisar ya yi fushi, a yayin zaman da majalisar dattijai ta yi a ranar Talata.

Sai dai a cikin wata tattaunawa da BBC, Ndume ya yi ƙarin bayani kan dalilansa na ficewa daga zauren majalisar lokacin da ake tafka muhawara kan lamarin da ya shafi rufe iyakokin Najeriya.

Ya ce: Lamarin ya samo asali ne “lokacin da Sanata Kawu Sumaila ya zo da ƙuduri wanda ya ce na gaggawa ne kan rufe iyakokin Najeriya da Nijar.

“Da farko an yi jayayya kan cewa ƙudurin ba na gaggawa ba ne, amma dai shugaban majalisa ya ce a bar shi ya ƙarasa abin da yake son faɗa.

“Bayan gama sauraron ƙudurin ne aka amince da cewa tun da abin ya shafi harkar tsaro a dakatar da shi,” in ji Sanata Ndume.

A cewarsa a daidai wannan gaɓar ne ya so ya fahimtar da majalisa da kuma shugabanta muhimmancin wannan ƙuduri, sai dai shugaban ya hana shi damar yin magana.

“So na yi na yi bayani kan cewa ƙudurin mai ƙarfi ne, amma a zahiri ya wuce ikon majalisar dattawan Najeriya.

“Domin rufe boda da aka yi ba shugaban Najeriya ne ya sa aka rufe ta ba, amma shi ne shugaban ECOWAS lokacin da abin ya faru, don haka zai iya kai kukanmu.

“Matuƙar za a warware wannan sai mun bi ta hanyar shugaban ƙasarmu, to ina so in yi masa bayani amma bai ba ni dama ba.

“Daidai lokacin da abin ya faru lokacin sallah ne, sai na tattara na fita, ashe ‘yan majalisa ‘yan uwana sun fahimci fitata ba daidai ba, kuma ‘yan jarida kuka sauya ma’anar fitata,” in ji Ali Ndume.

Ya ce sai da ya faɗa wa mataimakinsa cewa zai tafi ya yi sallah, sannan ya fita.

Amma daga baya ya koma cikin zauren majalisar ya kuma yi wa kowa bayani aka fahimci juna.

A yammacin ranar Talata ne kafafen yaa labaru suka ruwaito cewa Ali Ndume, mai wakiltar mazaar Majalisar dattijai ta kudancin Borno ya fice sanadiyyar fusata kan muhawarar da ake yi a zauren majalisa.

Rahotanni sun ce wata sa-in-sa da ta wanzu tsakanin Ndume da shugaban majalisar ne dalilin hakan.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake ganin cewa Ndume ya nuna rashin jin dainsa kan wasu lamurra na shugaban majalisar, Godswill Akpabio ba.

Ko a watan Agustan da ya gabata, sanata Ndume ya nuna rashin jin dain sa bayan da shugaban majalisar ya yi suɓul-da-bakan cewa an tura wa majalisar wasu kuɗaɗe gabanin tafiyar su hutu.

Kalamin da daga bayan Akpabio ya janye.

Ana dai kallon cewa akwai rashin jituwa tsakanin shugaban majalisar da kuma sauran mambobi.

A baya ma an riƙa yaɗa raɗe-raɗin cewar wasu ƴan majalisar dattijan sun yi yunƙurin kawo batun tsige shugaban majalisar.

Sai dai Ndume ya ce zai fi kyau ya bayar da gudumawa wajen gyara yadda ake tafiyar da lamarin majalisar a maimakon rushe shugabancinta, wanda shi me yake ciki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com