‘Yan Bindiga Sun Kashe Babban ‘Dan Kasuwa a Jihar Neja

 

Ana cikin jimami bayan maharan sun hallaka wani dan kasuwa a jihar Neja yayin da su ka afka masa a cikin shagonsa.

Marigayin mai suna Alhaji Samiu Jimoh ya gamu da tsautsayin ne bayan maharani sun yi kokarin tafiya da shi amma ya ki.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.

Jihar Neja – ‘Yan bindiga sun yi ajalin wani shahararren dan kasuwa Alhaji Abdul-Samiu Jimoh a karamar hukumar Mokwa da ke jihar Neja.

Daily Trust ta tattaro cewa marigayin ya rasa ransa ne bayan maharan sun kai masa hari a shagonsa da misalin karfe takwas na ranar Talata da ta gabata.

Meye ya jawo kashe dan kasuwar a Neja?

Majiyar ta tabbatar da cewa marigayin ya ki bin umarnin maharani ne na tafiya da shi wanda hakan ya yi sanadin rayuwarsa.

Wani mazaunin yankin, Idris Mohammed ya bayyana cewa dan kasuwar ya ki amincewa da su maharan su tafi da shi wanda ya sa su ka harbe shi.

Ya ce:

“Maharan sun harbi dan kasuwar ne bayan ya ki bin umarninsu na tafiya da shi inda su ka ce ma sa ya biyo su, a yayin cece-kucen ne su ka harbe shi.”

Wane martani ‘yan sanda su ka yi a Neja?

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kashe dan kasuwar ne a shagonsa na siyar da kayan mota.

Ya ce:

“A ranar 10 ga watan Oktoba da misalin karfe 9:45 na dare mun samu rahoton cewa ‘yan fashi da masu garkuwa sun kai hari shagon Alhaji Samiu Jimoh a shagonsa da ke kan hanyar Bida a Mokwa.”

Ya kara da cewa kafin zuwan jami’an ‘yan sanda wurin da lamarin ya faru, tuni har sun harbe dan kasuwar.

Abiodun ya ce sun kwashi dan kasuwar zuwa babban asibitin Mokwa inda daga nan ne aka tabbatar da cewa ya mutu.

Wannan na zuwa ne bayan ‘yan bindiga sun hallaka wasu mutum 12 da su ke aiki a wurin ma’adinai a kwanakin baya, cewar Channels TV.

‘Yan bindiga sun hallaka tsohon soja a Imo A wani labarin, ‘yan bindiga sun yi ajalin wani tsohon soja kuma mataimakin magatardar Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke jihar Ebonyi.

Marigayin mai suna Innocent Obi ya gamu da ajalinsa ne yayin da maharan su ka kai masa hari a gidansa da ke jihar Imo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com