Dalilin da Yasa Jam’iyyar PDP ta Dakatar da Jiga-Jiganta 2 a Jahar Borno
Babban jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, ta dakatar da jiga-jiganta biyu a jahar Borno.
‘Yan jam’iyyar da aka dakatar sun hada da tsohon dan takarar gwamna Mohammed Alkali Imam da tsohon shugaban PDP na jahar Zannah Gaddama Mustapha.
An dakatar da su ne domin suna janyo rabuwar kan a jam’iyyar kamar yadda sakatare Yusuf Mohammed Dikko ya sanar.
Jahar Borno – Rikicin cikin gida ya yi sanadin dakatar da manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP, biyu a jahar Borno, Daily Trust ta rawaito.
Read Also:
Wadanda aka dakatar din sun hada da tsohon dan takarar gwamna Mohammed Alkali Imam da tsohon shugaban PDP na jahar Zannah Gaddama Mustapha.
Dalilin dakatar da jiga-jiganta na PDP?
Daily Trust ta rawaito cewa Sakataren PDP na jahar Borno, Yusuf Mohammed Dikko, wanda ya sanar da dakatarwar yayin taron ‘yan jarida a Maiduguri ya ce wadanda aka dakatar din suna raba kan ‘yan jam’iyyar.
Ya ce jiga-jigan biyu duk sun ki amsa tambayoyin da aka yi musu dangane da korafin da shugabannin jam’iyyar na matakin mazabu da kananan hukumomi suka shigar a kansu.
Da aka tuntube shi domin ji ta bakinsa, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Borno, Mustapha ya ce jam’iyyar bata kafa kwamitin ladabtarwa ba domin yin bincike a kan lamarin.