Kano: Dalilin da Yasa PDP ta Janye da Zaben Kananan Hukumomi
Jam’iyyar PDP reshen jahar Kano ta sanar da janyewa daga zabukan kananan hukumomi na jahar.
Ta sanar da hakan ne a ranar Juma’a ga manema labarai ta hannun shugaban kwamitin rikon kwaryarta a jahar.
Ta ce tana da tabbacin ba za a yi zaben tsakani da Allah ba kuma salo ne na kwashe kudaden jahar da APC ta fito da shi.
Babbar jam’iyyar adawa a jahar Kano, PDP, karkashin bangarenta na Kwankwasiyya ta ce ta janye daga zabukan kananan hukumomi da za a gudanar a ranar 16 ga watan Janairu mai zuwa, Daily Trust ta wallafa.
Read Also:
Wannan hukuncin an sanar da shi ne a ranar Talata a yayin taron manema labarai wanda kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a jihar, wanda Dr. Danladi Albdulhameed tare da dan takarar kujerar gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, tare da sauran ‘yan Kwankwasiyya suka shirya.
Abdulhameed ya sanar da cewa jam’iyyar ta sakankance cewa “Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Ganduje ba za ta iya yin zaben gaskiya.”
Hakan yasa jam’iyyar PDP ba za ta shiga zaben da za a yi ba a ranar 16 ga watan Janairun 2021.
A bangaren kudi har naira biliyan 2.3 da aka ware domin zaben, PDP ta ce ba za ta shiga cikin harkallar da aka shirya domin kwashe kudin jihar Kano ba.