Dalilin da Yasa Rashawa ta yi katutu a Najeriya – Jonathan
Tshohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce rashin tabbas game da samun kulawa bayan yin ritaya ne ke rura wutar ayyukan rashawa tsakanin ma’aikatan gwamnatin ƙasar.
Jonathan ya bayyana haka ne ranar Talata a lokacin ƙaddamar da wani littafi game da rayuwar tsohon limamin cocin fadar gwamnatin tarayya, Obioma Onwuzurumba.
Read Also:
A cewar tsohon shugaban ƙasar “ɗaya daga cikin manyan matsalolin Najeriya, wanda ga dukkan alama shi ne ya sa rashawa ta yi katutu, shi ne mutane ba su san me zai faru da su ba gobe…shi ya sa irin waɗannan mutane kan ce tunda yanzu ina kan aiki bari na taimaka wa kaina ko ta halin ƙaƙa.”
Inda ya ƙara da cewa doka ba ta bai wa ma’aikata damar yin kasuwanci ko mallakar kamfanoni ba, sannan babu wanda zai kula da kai ko yaranka bayan ka bar aiki.
Daga nan sai ya buƙaci masu hali su samar da wani shiri na tallafa wa tsofaffi, domin a cewarsa hakan zai taimaka rage matsalar.