Mutane za su iya Shiga Cikin Haɗari Idan Suna Shiga Gasar Bidiyo na TikTok – NCC
Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa a Najeriya – NCC ta yi gargaɗin cewa mutane za su iya shiga cikin haɗari idan suna shiga cgasar bidiyo na TikTok, inda ta ce za su iya faɗawa tarkon masu satar bayanan jama’a ta intanet.
Read Also:
Hakan na kunshe ne a cikin shawarar da NCC ta bayar inda ta ƙara da cewa masu kutse a intanet za su iya amfani da gasar ta TikTok wanda ake kira ‘Invisible Challenge’ wajen yaɗa manhajar satar bayanai ta intanet da ake kira WASP ko W4SP.
Ta ƙara da cewa za a iya satar sunan mutum da lambobinsa na sirri da harkokinsa na kuɗi ta hanyar amfani da dabaru na zamba a intanet.
TikTok na da matukar farin jini a Najeriya musamman a tsakanin matasa.
Shafin TikTok shi ne na tara a farin jini a tsakanin shafukan soshiyal midiya a Najeriya kuma hukumomin ƙasar ba su sanya wa shafin ido ba.