Dalilin Taron Gwamnoni 36
Gwamnonin Jahohi za su yi wani zama a dalilin matsalar rashin tsaro.
Kungiyar NGF za ta zauna ne a Ranar Laraba bayan harin Zabarmari.
Gwamnan Kaduna da babban bankin CBN zasu yi jawabi wajen taron.
Vanguard ta ce gwamnonin jihohi 36 na kasar nan a karkashin kungiyar NGF za su zauna a gobe, 2 ga watan Disamba, 2020, a dalilin sha’anin tsaro.
Babban makasudin wannan taro shi ne gwamnonin su fito da sabon tsari a game da harkar tsaro.
A halin yanzu ana fama da yawan hare-haren ‘yan bindiga, ta’addancin Boko Haram da garkuwa da mutane da ake yi a jihohi da-dama a Najeriya.
Read Also:
Ana cikin wannan yanayi sai ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari a kauyen Zabarmari, jihar Borno, inda su kayi wa mutane har 43 yankan-rago.
Lamarin rashin tsaro yana damun jihohin kasar. Wannan zama da za ayi a ranar Laraba shi ne karo na 22 da kungiyar gwamnonin za ta zauna.
Daga cikin batutuwan da za a tattauna a zaman gobe, akwai kudirin ruwa da ya kawo ce-ce-ku-ce da Ministan harkokin ruwa zai yi karin-haske a kai.
Bayan jawabi daga Suleiman Hussein Adamu, takwaransa a ma’aikatar shari’a, Abubakar Malami zai bayyana inda aka kwana kan kudin harajin hatimi.
Haka zalika babban gwamnan CBN, Godwin Emefiele da gwamna Nasir El-Rufai za suyi magana kan yadda ake yin ayyuka da kudin asusun fansho.
Darektar NGF, Asishana Bayo Okauru, ta ce za a fara taron ne da karfe 2:00 na rana, amma gwamnoni za su samu damar hallara ta kafar gizo kafin nan.