Dalilin Tsadar Farashin Kayayyaki a Najeriya – Ministar Kudi
Hauhawar farashin kayayyaki na daga cikin matsalolin da ke ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya.
Ministar kudi, Zainab Ahmed, ta ce tsadar kudin dako da tafiye-tafiye ke haddasa matsalar hauhawar farashin kayayyaki.
Zainab ta ce gwamnati ta bullo da wani tsari da zai ragewa jama’a kudaden da suke kashewa wajen tafiye-tafiye da dakon kayansu.
Ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare,Zainab Ahmad,tace hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ta’allaƙa ne akan tsadar tafiye tafiye.
An samu ƙarin kuɗaɗen dako da tafiye tafiye a watanni da suka gabata sakamakon tashin gwauron zabi da man fetur ya yi, wanda shine sinadarin da yawancin ababen hawa da motocin haya ke amfani da shi.
Zainab ta fadi wannan magana ne lokacin tuntuɓar masana da masu ruwa da tsaki don tattaunawa akan tattalin arziƙi da tsarin kasafin kuɗi don tallafawa direbobi daga ma’aikatar kuɗi a shekarar 2020.
Ta ce tsarin daftarin dokar zai rage tsadar kudin dako da tafiye tafiye a faɗin ƙasar.
Kuɗin dako da tafiye tafiye da jama’a suke biya yana ƙaruwa da kaso 12.7% duk wata, sannan kuma yana ƙaruwa da kaso 48.02% duk shekara.
Wannan shine abin da alƙaluman da aka tattara, kamar yadda alƙaluman hukumar kididdiga da tattara alƙaluma ta ƙasa (NBC) suka nuna.
Read Also:
Zainab ta ce dokar ta zo da sabbin tsare tsare ma su ƙayatarwa, ta bada misalin “kasafin kuɗi don matafiya” wanda aka tsara shi don tallafawa tare da rage raɗaɗin matafiya ta hanyar bibiyar tsarin tafiye-tafiye.
Ministar ta ce “Babban dalilin da yasa mukayi haka, shine mun fahimci tsadar dako da tafiye tafiye na daga cikin jigon abubuwa masu haddasa tsada a tattalin arziƙi.
“Idan ku ka yi duba da yanayin hauhawar farashi, kuma ku ka binciki dalilin hauhawar, za ku ga cewa gundarin dalilin hauhawar farashin ya ta’allaƙa akan farashin dako.
“A nan, manufarmu itace mu rage kuɗin dako da tafiye tafiye domin sauƙaƙa kasuwanci don farashin kaya ya ragu gun masu siye.”
Yanayin hauhawar farashin kayayyaki a ƙasa ya ƙaru zuwa kaso 13.71% a watan Satumba daga kaso 13.22 a watan baya, a ƙiddidigar NBS.
Masu hasashe daga FDCL (Financial Derivatives Company Limited) sun ce an kimanta hauhawar farashin kayyaki da kaso 14.5 a watan Oktoba daga kaso 13.7 a watan Satumba.
“Hakan na nufin hauhawar farashin zai kai kimanin watanni 14. Zai kuma kai ƙololuwar mataki a watanni 33.
“Kayan abinci sune za su fi komai hauhawa inda akayi ƙiyasin zasu hau da kaso 17.05. Sauran kayayyakin amfani suma ana tsammanin zasu iya kaiwa haka,” a cewarsu.
Gwamnan Babban bankin ƙasa, Mr Godwin Emefiele, ya yi magana, kwanan nan, a kan cewar hauhawar farashin kayayyaki da kuma ƙankancewar tattalin arziƙi ya janyo hanƙoron yin sabbin tsare-tsare da kuma buƙatar ƙarfafa sarrafa kayyaki don bunƙasar tattalin arziƙi.