Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla ya Gargadi ‘Yan Bindigan Jahar Zamfara
Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla, babban limamin masallacin Juma’a na Sambo Dan Asafa da ke Gusau ya gargadi ‘yan bindigan jahar.
Sheikh Dalla-Dalla yayin hudubarsa na ranar Juma’a ya shaidawa ‘yan bindigan cewa fushin Allah zai sauka a kansu idan ba su tuba ba.
Babban malamin ya yi gargadin cewa zubar da jinin mutane babban laifi ne kuma ya bukaci al’ummar jahar su cigaba da addu’a domin Allah ya magance musu matsalar.
Babban limamin masallacin Juma’a na Sambo Dan-Ashafa da ke Gusau, Sheikh Abdullahi Dalla-Dalla, a ranar Juma’a ya gargadi ‘yan bindigan da ke jahar su janye ko su gamu da fushin Allah, Daily Nigerian ta rawaito.
Read Also:
A yayin hudumar Juma’a da ya yi, ya ce kashe mutane da keta hakkinsu a jahar zai haifar da fushin Allah, idan har masu aikata laifin ba su tuba sun dena ba kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.
Dalla-Dalla ya ce:
“Abin da na ke kira ga ‘yan bindigan shine su tuba; su dena kashe mutanen da ba-su-ji-ba-ba su gani ba sannan su mika mukamansu kafin fushin Allah ya sauka a kansu.
“Wannan babban abun damuwa ne ga masu ruwa da tsaki. A matsayin mu na musulmi, mu cigaba da yin addu’o’i.
“Mu yi addu’ar ga Allah mu nemi taimakonsa game da kallubalen tsaro da ke kara tabarbarewa a jahar.”
Jahar Zamfara na daga cikin jahohin da hare-haren yan bindigan ya tsananta.
Hakan ya shafi noma da kasuwanci saboda yadda yan bindigan ke zuwa su sace mutane a gonaki ko kai hari a ƙauyukan.
A shekarar 2019 gwamantin jahar Zamfara ta yi yarjejeniyar sulhu da yan bindigan.
Sai dai duk da hakan har yanzu ana ci gaba da kai hare-haren kuma ana sace mutane ko halaka su.