Mafarauta Sun Kashe ‘Yan Bindiga 47 a Jahar Niger

 

Mafarauta sun yi nasarar kashe yan bindiga kimanin guda 47 a kananan hukumomin Shiroro da Rafi a jahar Niger.

Mafarautan sun kai wa yan bindigan harin bazata ne a wani mabuyarsu da ke garin Magami suka yi nasarar cin galaba a kansa.

A baya-bayan nan ne Gwamna Abubakar Sani-Bello na jahar Niger ya kafa wata kungiyar yan banga na musamman don yakar yan bindigan.

Mafarauta sun kashe a ƙalla ƴan bindiga 47 da ke adabar garuruwan da ke karamar hukumar Shiroro ta Jahar Niger, PRNigeria ta rawaito.

Mafarauta, yayin wani harin bazata da suka kai garin Magami da ke tsakanin ƙananan hukumomin Shiroro da Rafi, a ranar Laraba sun kashe yan bindigan a ranar Laraba.

Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa yan bindiga sun dade suna fakewa a garin da ke kusa da rafi.

Majiya daga hukumar tsaro ta tabbatar da kashe ‘yan bindigan

Wani jami’in ɗan sanda na sirri wanda baya so a ambaci sunansa ya tabbatar cewa yan bindigan da dama sun tsere da raunin bindiga baya da waɗanda aka kashe.

Ya ce:

“Zan iya tabbatar maka cewa yan bindigan sun hadu da ajalinsu. Mafarautan sun kashe a ƙalla 47 daga cikinsu.”

PRNigeria bata iya tabbatarwa ba ko mafarautan na cikin yan banga na musamman ta NSVC da gwamnatin jahar Niger ta kafa a jahar don tallafawa hukumomin tsaro.

Yayin rantsar da su a Yunin 2021, Gwamna Abubakar Sani-Bello na jahar ya ce ba za su bari ƴan bindigan su yi musu barazana ba ko su sauya musu tsarin rayuwarsu.

Mr Sani Bello ya ce:

“Yan bindigan suna son tilasta mana sauya tsarin rayuwarmu a Jahar Niger amma ba za mu ƙyalle su ba.

“Sun hana yaran mu zuwa makaranta, sun hana mu tafiya a tituna, sun hana manoma zuwa gonaki yanzu suna neman hana mu komai, amma ba za mu gajiya ba. Ba za mu bari hakan ya faru ba; za mu cigaba da rayuwar mu yadda muka saba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here