Cutar Kwalara ta yi Ajalin Mutane 104 a ƙasar Nijar

Hukumomi a Nijar sun tabbatar cewa cutar kwalara ta yi ajalin mutum 104 a ƙasar.

Ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta bayar da rahoton cewa mutum 2,874 suka kamu da cutar a jahohin Niamey da Maradi da Zinder da Dosso da Tahoua da kuma Tillaberi.

Ministan lafiya na ƙasar Illiassou Mainassara ya kuma tabbatar da cewa mutane shida da suka kamu da cutar korona nau’in Delta a Nijar sun warke.

Ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa dukkaninsu wadanda ke Yamai babban birnin ƙasar, an yi masu magani amma ya bayyana damuwa kan yaɗuwar cutar a ƙasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here