Wani Dan Wasan ƙwallon ƙafa ya Rasu – Yusuf Usman Usein

 

Yusuf Usman Usein da ke buga wa Shooting Stars da Crown FC wasan ƙwallon ƙafa ya rasu.

Ɗan wasan da ke buga gaba ya tafi yana wasa da Gateway na Abeokuta ne sai ya yanke jiki ya faɗi.

A safiyar ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba ne Crown FC ta tabbatar da cewa Usein ya rasu.

Ɗan ƙwallon Najeriya, Usman Yusuf, da ke buga wa ƙungiyar Crown Football da ke Ogbomoso, Oyo wasa ya rasu.bayan ya yanke jiki ya faɗi yayin da suke buga wasa a Abeokuta a jihar Ogun.

Abin baƙin cikin ya faru ne a ranar Lahadi 15 ga watan Nuwamban 2020 a filin wasa na Muda Lawal, Asero, Abeokuta.

Yusuf wadda ke gwaji a Gateway United FC, ya buga kashi na farko na wasar da suke buga wa da Sliema Wandarers kafin afkuwar lamarin.

An ruwaito cewa likitocin da ke filin wasa sun farfaɗo da shi bayan ya yanke jiki ya faɗi. Daga nan aka garzaya da shi asibiti inda daga bisani ya rasu.

Moses Ojewumi, jami’in watsa labarai na Gateway FC ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Litinin a Abeokuta.

Ya ce, “Usman Yusuf wanda ya zo gwaji ya buga kashi na farko na wasan da Gateway United FC ke bugawa da Sliema Wandarers a ranar Lahadi, a farko ya nuna alamu marasa kyau kuma likitan Gateway United ya duba shi.

“A daren ranar labari ya zo cewa rashin lafiyar ya sake dowowa, nan take aka kai shi asibitin Jihar inda ya rasu a can.

” Ojewumi ya ƙara da cewa ɗan wasan bai nuna alamun bashi da lafiya ba lokacin da ya zo gwajin kuma bai mutu a sansanin bada horon wasa ba kamar yadda wasu suka yi kuskuren bada rahoto.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here