An Yankewa Wani Dan Majalisa Hukuncin Zaman Gidan Yari

Cece-kuce ya barke, bayan an yankewa wani dan majalisa hukuncin zaman gidan gyaran hali.

An yanke wa Hercules Okoro hukuncin ne sakamakon zarginsa da akeyi da cin zarafi.

Kotu ta zargesa da cin zarafin mataimakiyar kakakin majalisa, duk da ya musa zargin.

An yankewa dan majalisar jihar Imo, Hercules Okoro, mai wakiltar mazabar Ohaji Egbema, hukuncin zama a gidan gyaran hali akan laifin cin zarafi.

Legit.ng ta tattara bayanai akan yadda aka kama Okoro, dan majalisa a karkashin jam’iyyar APC, a ranar 13 ga watan Nuwamba, bayan wani rikici da ya barke tsakaninsa da mataimakiyar kakakin majalisar tarayya, Amarachi Iwuanyanwu.

An adana Okoro a gidan gyaran halin ne saboda laifuka 8 da ake zarginsa da aikatawa. Duk da dai bai amsa laifin da ake zarginsa da su ba.

Duk da lauyansa, Amandibuogu Osondu ya nemi belinsa amma abin yaci tura. A cewarsa laifin bai kai a dauresa ba. Alkalin, T Okee yace zai bukaci wani lokaci kafin ya duba yuwuwar bayar da belinsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here