Ribar N71.2bn a Sa’o’i 24: Aliko Dangote ya Shiga Jerin Manyan Attajirai 100 na Duniya
Shahararren ɗan kasuwa Aliko Dangote ya samu ribar naira biliyan 71.2 a cikin sa’o’i 24.
Hakan ya bai wa Dangote damar shiga cikin jerin manyan attajirai 100 da suka fi kowa kuɗi a duniya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da farashin simintin kamfanin na Dangote ya yi rashin gwauron zabi a kasuwar hada-hadar hannun jari.
Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aliko Mohammed Dangote, ya ci gaba da ƙara samun ƙarfi a matsayin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afrika yayin da ya shiga jerin masu kuɗi 100 na duniya.
Wasu bayanai da Legit Hausa ta samu daga shafin Bloomberg, ya nuna cewa ɗan kasuwar ya yi nasarar shiga cikin manyan attajirai 100 na duniya sakamakon ribar da ya samu a kasa da sa’o’i 24.
Dangote a jerin manyan attajiarai 100 na duniya
A ranar Litinin, 11 ga watan Satumba ne dai ɗan kasuwar ya samu ribar da ta kai dala miliyan 96.2 sakamakon rashin farashin simintinsa da aka samu.
Read Also:
Ma’aikatar simintin Dangote dai ita ce ta fi kowace girma a nahiyar Afrika, wacce ke ci gaba da riƙe shi a cikin manyan masu kuɗin duniya tun shekaru 12 baya zuwa yanzu.
Simintin na Dangote ne dai aka fi hada-hadarsa a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya a ranar Litinin, a kan naira 365 duk guda ɗaya.
Haka nan kuma kamfanin na simintin Dangote shi ne ya fi kowane kamfani samun riba a Najeriya.
Manyan ‘yan kasuwar Najeriya sun tafka gagarumar asara
Legit a baya ta yi rahoto kan gagarumar asarar da ‘yan kasuwa da dama suka tafka daga farko-farkon shekarar nan zuwa yanzu.
Abdulsamadu Isiyaka Rabiu na kamfanin BUA, da kuma Mike Adenuga mai kamfanin Globacom sun tafka mummunar asara su ma a cikin wannan shekara ta 2023.
Ko shi kanshi Alhaji Aliko Dangote sai da ya yi gagarumar asarar da ta sauko da shi daga matsayin wanda ya fi kowa kuɗi a Afrika kafin daga bisani ya dawo da kambun na sa.
Har yanzu Dangote bai fara tace man da ake bukata a Najeriya ba
Legit Hausa a baya ta fitar da wani rahoto kan cewa har yanzu matatar man Aliko Dangote da aka yi alƙawarin cewa za ta riƙa tace man fetur da ake buƙata a cikin ƙasa, ba ta fara aikin ba.
Ana bukatar man da ya kai aƙalla ganguna 650,000 a kowace rana a Najeriya, wanda alamu ke nuni da cewa ko kaso 10% na abinda ake buƙata ma’aikatar ba ta fara tacewa ba.