Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Arc Yomi Awoniyi ya Fice Daga PDP Zuwa APC

 

Yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Kogi, jam’iyyar APC ta yi babban kamu daga babbar jam’iyyar adawa PDP.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Arc Yomi Awoniyi, ya shiga jam’iyyar APC a hukumance ranar Talata a hedkwata da ke Abuja.

Gwamna Yahaya Bello ya yaba wa Awoniyi, inda ya ce wannan alama ce ta mutane sun gamsu da gwamnatin APC.

FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kogi, Arc Yomi Awoniyi, ya tabbatar da koma wa jam’iyyar APC a hukumance gabanin zaɓen gwamnan jihar ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Awoniyi, wanda ya nuna gansuwarsa da gwamnatin Yahaya Bello, an karbe shi a hukumance zuwa inuwar APC a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, ranar Talata.

FCT Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kogi, Arc Yomi Awoniyi, ya tabbatar da koma wa jam’iyyar APC a hukumance gabanin zaɓen gwamnan jihar ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Awoniyi, wanda ya nuna gansuwarsa da gwamnatin Yahaya Bello, an karbe shi a hukumance zuwa inuwar APC a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja, ranar Talata.

Ya rike mukamin mataimakin gwamnan jihar Kogi daga 2011 zuwa 2015 a lokacin gwamnatin Captain Idris Wada, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Meyasa ya zaɓi shiga jam’iyyar APC?

Tsohon jigon jam’iyyar PDP ya aminta cewa siyasar Kogi tana da sarkakiya da kalubale, ya kuma yabawa Gwamna Yahaya Bello bisa yadda ya bai wa mara ɗa kunya.

Mista Awoniyi ya ce:

“Na yi aiki a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kogi tsakanin 2011 zuwa 2015. Na san jihar sosai, kuma zan iya gaya muku cewa gwamna mai ci yanzu ya yi fice sosai ta fuskar jagoranci da shugabanci nagari.”

“Wadannan halaye da nagarta na daga cikin dalilan da suka ja hankalina na yanke shawarar shiga APC domin na goya masa baya da kuma gwamnati mai zuwa.”

Gwamna Yahaya Bello ya yaba da matakin Da yake maraba da Awoniya, gwamna Yahaya Bello wanda ya ayyana shi a matsayin “Babban kifi” ya ce matakin da ya ɗauka na shiga APC shi ne ya dace.

Ya jaddada cewa matakin Awoniyi ya nuna karara yadda jama’a suka gamsu da nasarorin da ya samu da kuma yadda suke nuna goyon baya ga shugabancinsa domin ci gaban jihar.

A rahoton Tribune Online, Gwamnan ya ce:

“Ina mai farin cikin maraba da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Arc Abayomi Awoniyi zuwa jam’iyyar mu a yau. Awoniyi fitaccen mutum ne da ya shigo tafiyar mu a APC.”

“Na ji dadin matakin da ya ɗauka na shiga jam’iyyar mu, kuma ina mai tabbatar muku da cewa jam’iyyar APC za ta kara yi wa al’ummar jihar Kogi tulin ayyuka.”

Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba wa tsohon mataimakin gwamna bisa sauya sheƙar da ya yi zuwa APC.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com