Gwamna Akeredolu ya Kori Dukkan Hadiman Mataimakinsa

Alaka na kara tsami yayin da Gwamna Akeredolu ya kori dukkan hadiman mataimakinsa.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya shafe watanni ya na jinya a kasar Germany.

Kafin dawowarsa a wannan mako, an samu takun saka tsakanin mataimakin gwamnan da na kusa da gwamnan.

Jihar Ondo – Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya sallami dukkan hadiman mataimakinsa, Lucky Ayedatiwa.

Korar hadiman na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta bakin sakataren yada labaran gwamnan, Richard Olatunde a yau Talata 12 ga watan Satumba.

Wannan na zuwa yayin da ake tunanin akwai takun saka tsakanin gwamnan da mataimakinsa. Daily Trust ta tattaro cewa korar hadiman na daga cikin shirin wargaza dukkan mukamai a jihar.

Bayan korar hadiman, an umarci ma’aikatar yada labarai ta ci gaba da kula da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com