‘Dan Kwallon Kafa ya Yanke Jiki ya Fadi, Ya Mutu Ana Tsaka da Buga Wasan
Wani matashi dan Najeriya ya yanke jiki ya fadi matacce a daidai lokacin da yake tsaka da buga tamola.
Mutumin mai shekaru 31 bai samu taimakon gaggawa ba lokacin da abun ya faru domin abokan wasansa sun zata hutawa yake yi har sai da suka ji shirun yayi yawa.
Rundunar yan sandan jihar Lagas ta tabbatar da faruwar al’amarin wanda ya wakana a yankin Lekki.
Lagos – Wani matashi mai shekaru 31 ya yanke jiki ya fadi matacce yayin da yake tsaka da buga kwallo a yankin Lekki na jihar Lagas.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan mummunan al’amarin ya afku ne a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba.
An tattaro cewa matashin wanda ba a tabbatar da sunansa ba yana bin kwallo ne lokacin da ya yanke jiki ya fadi.
Read Also:
Rahoton ya kuma kawo cewa marigayin bai samu taimakon gaggawa ba domin sauran abokan wasansa sun zata yana kokarin daidaita numfashinsa ne.
An kuma rahoto cewa sauran abokan wasan nasa da suka shafe tsawon mintuna 30 suna jiran ya dawo cikinsu sun je daga shi a gefen filin wasan da ya kwanta kawai sai suka gano cewa sam baya motsi.
Wani dan kwallo, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ndubisi, ya ce an tabbatar da mutuwarsa ne a wani asibiti da aka kai shi. Kakakin yan sandan jihar Lagas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da cewar dan kwallon ya yanke jiki ya fadi yayin da yake buga tamola.
Hundeyin ya shawarci jama’a da su daina ketare iyaka sannan su huta a duk lokacin da suka ji gajiya. rahoton Vanguard.
Ya ce:
“Kada ku wuce kima. Idan kun gaji, samu wuri ku huta. Bugu da kari, ku dunga zuwa ganin likita lokaci zuwa lokaci. Kamar yadda masu iya zance kan ce, ‘rai daya ne bashi da na biyu.”