‘Dan Sandan da Bai Taba Karbar Cin Hanci ba, Zai Ajiye Aiki
Bayan shekaru 30, DSP Francis Erhabor na son fita daga hukumar yan sanda.
Erhabor ya bayyana bacin ransa kan irin cin fuska da rashin adalcin da ake yi masa.
Ya shahara da lakabin wanda bai taba karban cin hanci ba a rayuwarsa.
Francis Erhabor, DPO na Itam, jihar Akwa Ibom, wanda akwa ruwaito ya ki karban cin hancin N864m a cikin shekaru uku, na tunanin ajiye aikin saboda rashin adalcin da ake masa.
Read Also:
A ranar Asabar, an samu rahotannin cewa DSP Erhabor ya yi murabus daga aikin yan sanda saboda wasu miyagu dake hanashi cigaba a hukumar.
Rahotannin sun bayyana cewa jami’in ya ajiye aikin ne saboda yadda ake karawa sa’o’insa girma amma shi yana waje daya.
Amma daga baya an samu labarin cewa bai yi murabus ba tukun amma yana tunanin yin hakan shi yasa ya dauki hutun kwanaki uku domin yanke shawara, The Cable ta ruwaito.
Jami’in dan sandan ya cika aikin tun shekarar 1990.