Yadda ɗan Takarar Gwamnan PDP ya ci Dukan Tsiya a Hannun ‘Yan Daban Siyasa

Yan daban siyasa sun sa bulala sun zane ɗan takarar gwamnan PDP a Ogun, Segun Showunmi, a kusa da Kotu.

Rahoto ya nuna lamarin ya faru yau Litinin yayin da Kotun ke haramar fara zaman sauraron ƙara kan zaben Gwamna.

An tattaro cewa jami’an tsaro na kallon ‘yan daban amma ba su musu komai ba har lokacin da tsohon ɗan takarar ya isa wurin

Ogun – ‘Yan daban siyasa ɗauke da sanduna da bulala sun lakaɗa wa tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a inuwar jam’iyyar PDP, Segun Showunmi, dukan tsiya a kusa da Kotu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan daban sun zane ɗan siyasan ne yayin da Kotun sauraron karar zaben gwamnan Ogun ta fara zaman shari’a a Abeokuta ranar Litinin.

Kotun zaɓen ta fara zama sauraron ƙarar da ɗan takarar gwamnan PDP a zaben 2023, Ladi Adebutu, ya kalubalanci nasarar gwamna Dapo Abiodun na jam’iyyar APC.

An ce titin zuwa wurin da aka ware wa Kotun a harabar Kotun Majistire da ke Isabo, zagaye yake da jam’ian tsaro amma duk da haka sai da ‘yan daba suka mamaye wurin don nuna goyon baya ga jam’iyyunsu.

‘Yan daba sun kaure da faɗa a Farko

An hangi wasu daga cikin tsagerun ‘yan daban riƙe da bulalu yayin da rikici ya kaure tsakanin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki da PDP mai adawa.

Lamarin ya rincaɓe har sai da jami’an tsaro da suka ƙunshi dakarun ‘yan sanda, DSS da civil Defence suka shiga tsakani sannan aka samu nasarar raba faɗan da tarwatsa ‘yan daban.

Duk da ‘yan daban ka ɗauke na bulalu a hannunsu, jami’an tsaron ba su ɗauki wani mataki na kare aukuwar yamutsi a wurin ba, sai suka zuba musu ido.

Yadda ɗan takarar PDP ya ci dukan tsiya

Jaridar Punch ta ce tsohon ɗan takarar gwamnan PDP, Mista Showunmi, ya dira bakin kofar shiga kotun a daidai lokacin da ‘yan daban ke tsaye suna kallon masu shiga.

Da zuwansa ya gabatar da kansa ga jami’an tsaron da ke gadin babbar Kofa, ba zato ‘yan daban suka ce da wa Allah ya haɗa su, suka kama bugunsa da sanduna da bulalai.

Rahoto ya nuna wasu ne suka kwace shi suka gudu da shi, bayan nan kuma ‘yan daban suka haɗa da mambobin jam’iyyun siyasa suka lakaɗa wa na jaki a wurin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com