Datse Layukan Sadarwa a Jahohin Arewa Maso Yamma na Barazana ga Kasuwanci

 

Rahoton SBM ya ji ta bakin jama’a mazauna jahohin Zamfara, Katsina da Kaduna kan datse layikan sadarwa.

Kamar yadda wadanda aka ji ta bakinsu suka bayyana, sun koka da yadda kasuwancinsu suka durkushe a cikin kwanakin nan.

Amma sai dai, mazauna jahohi Zamfara da Katsina sun jinjina wa gwamnati kan yadda tsaro ya inganta a yankunansu.

Kasuwanci ne a halin yanzu ke jin tsanani kan hukuncin gwamnati na datse layikan sadarwa a wasu jahohin arewa maso yamma na kasar nan kamar yadda rahotannin SB Morgan suka bayyana, TheCable ta rawaito.

Rahotan mai taken; “Hostile reception – The impact of telephony shutdowns in North-West Nigeria,” wanda aka bincike mutum 679 a makon tsakiyan watan Satumban 2021 domin duba abinda datse kafofin sadarwa suka janyo.

A ranar 3 ga watan Satumba, an bukaci hukumar sadarwa da ta bai wa kamfanonin sadarwa umarnin datse sabis a Zamfara domin shawo kan miyagun al’amuran ‘yan bindiga.

Jahohi kamar Katsina da Sokoto sun bi sahun datse layikan sadarwan a wasu kananan hukumominsu, TheCable ta wallafa.

Wannan hukuncin datse layikan sadarwan a wasu jahohin ya janyo cece-kuce daga jama’a.

Daga binciken, an samu ra’ayoyin mutum 238 a Kaduna, 234 daga Katsina da kuma 207 daga Zamfara.

Abinda binciken ya samo ya bayyana cewa dukkan mazauna Zamfara ba su samun damar amfani da layikan wayoyi, kashi 13 na jama’ar Kaduna ba su samun damar amfani da layikan yayin da kashi 3 na Katsina basu samun damar amfani da layikan.

A bangaren kasuwanci, kashi 61 na wadanda aka tattauna da su a Zamfara ba su iya amfani da sabis kuma sun ce hakan ya matukar taka rawa wurin dakile al’amuran kasuwancinsu yayin da sauran suka ce illa kadan hakan yayi musu.

A Kaduna, kashi 62 daga cikin wadanda aka zanta da su ba su amfani da sabis sun ce wannan umarni bai wani takura su ba da kasuwancin, yayin da kashi 29 suka ce hakan ya matukar lalata musu kasuwanci.

A Katsina, kashi 57 na wadanda aka zanta da su kan rasa sabis sun ce umarnin ya dan taba su da kasuwancin su yayin da kashi 14 suka ce sun fuskanci matsanciyar takura da kuma matsala a kasuwancinsu.

A bangaren tsaro kuwa, kashi 43 na wadanda aka zanta da su a Zamfara sun ce harkar tsaro ta inganta tun bayan datse sabis, yayin da kashi 18 na Kaduna da kashi 14 na Katsina suka ce tsaro ya inganta a jahohin su.

Rahoton ya kara gano cewa, kasuwanci a Zamfara ne suka fi durkushewa saboda tattalin arzikin ta fiye da Kaduna da Katsina.

“A yankin da tuni ya ke fama da matsalar fatara, yanzu haka mazauna yankin na siyan abubuwa a farashi mai tsada saboda luguden da sojoji ke yi wa ‘yan bindiga,” rahoton yace.

“Wannan halin matsin rayuwa da ake ciki yasa muke ta kira da a hakura da datse sabis domin mazauna jahar su koma kasuwancin su kuma hukumomin tsaro su duba cigaban da aka samu.

“Daya daga cikin abubuwan da ke assasa rashin tsaro a arewa maso yamma shi ne talauci.Duk wani mataki da aka dauka wanda ya bayyana karuwar matsin rayuwa dole ne ya kasance na gajeren lokaci don kada a kara wani matsin ga jama’a.

Wani abu kuma da datse sabis shi ne rashin sanin halin da sojoji suke ciki ko kuma yadda ayyukan su ke cigaba. Labarai a yankin arewa maso yamma sun yi karanci kuma umarnin da aka bada ya na daidai da na datse kafofin yada labarai.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here